Connect with us

Labarai

Gwamnan Jigawa Ya Bada Umarnin Zaftare Farashin Kudin Taki

Gwamnatin jihar Jigawa ta sayo buhunan takin zamani guda dubu 120,000, wanda za’a rabawa wuraren saida takin guda 43 dake fadin jihar, kuma za’a sayar dasu akan naira 16,0000 akan kowacce buhu.

Gwamnan jihar Malam Umar Namadi ne ya bayyana haka lokacin da ya gana da kwamitin rabon kayayyakin a yammacin ranar Juma’a a gidan gwamnati na Dutse.

Namadi ya yi gargadi game da karkatar da takin da gwamnati ke son a sayar wa manoma a farashi mai rahusa.

Ya yi kira ga mambobin kwamitin da su sa ido kan yadda za a sayar da takin da aka baiwa manoma a fadin jihar domin noman damina na shekarar 2023.

Gwamnan ya bukaci mambobin kwamitin da su kara himma da kwazo don ganin cewa kayayyakin sun isa ga manoman da aka yi niyya akan farashi mai rahusa.

“Dole ku sauke nauyin da aka dora muku bisa gaskiya da rikon amana. Duk wanda aka samu yana hada baki da wata kungiya ko wani mutum don karkatar da kayan, za a hukunta shi,” inji shi.

Ya ce gwamnatinsa ta kuduri aniyar samar da kayayyakin noma ga manoman da suka taso a jihar Jigawa.

A wata hira da Daily Trust tayi a ranar Lahadi, wani manomi mai suna Suleiman Muhammad Desina, ya ce “Mun yi matukar farin ciki da Gwamna Namadi ya rage kusan Naira 9,000 na buhun taki wanda hakan ke nufin yanzu za mu iya biya.”

Ya ce manoma a ko da yaushe suna cikin rudani a duk lokacin da damina ta zo saboda tsadar takin da kayan noma.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet