Labarai
Ta Tabbata Babu Ganduje, Da Wasu Jiga-jigan APC Cikin Ministocin Tinubu

Wasu jiga-jigan jam’iyyar (APC) mai mulki, APC da ake sa ran za su shiga majalisar ministocin shugaban kasa, Bola Tinubu, sun bace a cikin jerin ministocin da aka bayyana a ranar Alhamis.
Jaridar DAILY POST a baya ta rahoto cewa shugaban majalisar dattawa, Goodwill Akpabio ya karanta jerin sunayen a ranar Alhamis kamar yadda fadar shugaban kasa ta mika wa zauren majalisar Sunayen.
Femi Gbajabiamila, tsohon kakakin majalisar wakilai kuma a halin yanzu shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa ne ya mika jerin sunayen ga Akpabio.
Sai dai sabanin rade-radin da ake yi na cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje da sauran jiga-jigan jam’iyyar da suka yi yakin neman nasarar Tinubu a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu, ba a saka su cikin jerin sunayen ba.
Sunayen tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, tsohon ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Festus Keyamo da wasu jiga-jigan jam’iyyar ba a cikin jerin sunayen da aka dade ana jira.
Har ila yau, jerin sunayen sun kawo rugujewar rade-radin cewa wanda shugaba Tinubu ya nada a matsayin minista daga jihar Binuwai zai fito daga mazabar Benuwe ta Kudu.
Wasu sunaye har zuwa yanzu basa a cikin jerin sunayen wadanda aka zaba daga jihar.
Duk da haka, a cewar wasikar Tinubu zuwa Majalisar Dattawa, za a iya samun karin wasu ministoci daga baya.