Connect with us

Labarai

Zamfara: Wasu Mata Hudu Da Aka Yi Garkuwa Da Su Sun Samun ‘Yanci

 

Wasu Mata hudu da ‘yan bindiga suka sace a jihar Zamfara watanni shida da suka gabata sun samu ‘yanci.

Idan dai ba a manta ba ‘yan fashin sun sace matan hudu ne watanni shida da suka gabata inda suka yi barazanar aurensu idan har suka kasa biyan kudin fansa Naira miliyan 12.

Da take zantawa da jaridar PUNCH ta wayar tarho, wata uwar guda daya daga cikin ‘yan matan da ta bukaci a sakaya sunanta ta ce ‘yan bindigar sun sako matan kuma a halin yanzu suna karkashin kulawar jami’an tsaro don duba lafiyar su.

Ta ci gaba da cewa har yanzu ba su hadu da wadanda abin ya shafa ga iyalansu ba.

Ta ce, “Jami’an tsaro sun kira ni suka ce min an kubutar da ‘yata daga hannun ‘yan fashin kuma tana karkashin kulawarsu.

“Na yi magana da ‘yata a waya wacce ta tabbatar min da hakan, suna jinya a asibiti”.

Kokarin samun jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar SP Yazid Abubakar ya ci tura saboda an kasa samunsa ta wayar tarho.

A halin da ake ciki, wani masani kan yaki da ta’addanci, Zagalola Makama ya sanar a shafinsa na Twitter cewa an sako wasu mata hudu.

Makama ya kara da cewa suna kwantar da su a asibiti ana duba lafiyarsu.

Ya ce, “Wadancan matan da aka sace sun samu ‘yancinsu daga hannun ‘yan bindiga a Zamfara.”

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet