Featured
Mun shirya tsaf don tafiya yajin aiki a ranar Laraba – NLC

Ƙungiyar Ƙwadago a Najeriya NLC ta ce ba bu gudu ba bu ja da baya wajen tafiya yajin aikin da ta tsara gudanarwa a ranar Laraba.
Ƙungiyar na ci gaba da mayar da hankali wajen haɗa kan ma’aikata don ganin an tafi yajin aikin nan da kwanaki biyu masu zuwa.
Matakin hakan ya biyo bayan tashi baram-baram da ƙungiyar ta yi bayan wani zama da wakilan gwamnatin tarayya a Abuja.
A baya ƙungiyar ta shirya tafiya yajin aikin, sai dai ta janye daga baya bayan sulhu da aka yi da bangaren gwamnatin tarayya.