Labarai
Tsaro: Ribadu Ya Shiga Wani Taron Sirri Da Wasu Gwamnonin Biyar

Nuhu Ribadu, mai baiwa shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin tsaro ya yi wata ganawar sirri da gwamnonin jihohin Kudu maso Gabas biyar a Abuja ranar Litinin din nan.
Duk da cewa ba a bayyana ajandar taron sirrin ga manema labarai ba, amma watakila bai rasa nasaba da yadda matsalar tsaro ke kara tabarbarewa a jihohin Anambra, Enugu, Abia, Imo da Ebonyi.
A ranar Larabar da ta gabata ne Majalisar Dattawa ta yi Allah-wadai da zaman da aka yi a ranar Litinin a shiyyar Kudu maso Gabas.
Majalisar ta kuma nemi Gwamnatin Tarayya da ta hada kai da Gwamnatin Finland tare da mika wani mai fafutukar kafa kasar Biafra, Simon Ekpa, domin gurfanar da shi gaban kuliya.
Majalisar dattijai ta yanke shawarar gayyatar Ministan Harkokin Waje (lokacin da aka nada shi) da masu ruwa da tsaki don gudanar da cikakken bincike tare da gabatar da sauran masu daukar nauyin wannan lamari.
Majalisar dattawan ta kuma yi watsi da shawarar a saki shugaban kungiyar ta IPOB, Nnamdi Kanu, inda ta ce hakan zai kai ga yanke hukunci saboda har yanzu maganar sakin sa na gaban kotu.
An ce wani bangare na masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) ne ke aiwatar da dokar zaman gida ba bisa ka’ida ba a jihohi biyar na Kudu maso Gabas.
A shekarar 2021 ne aka ayyana dokar da ta sabawa kundin tsarin mulkin kasar, domin a matsa bukatar a saki shugaban kungiyar ta IPOB, Nnamdi Kanu, wanda hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ke tsare da shi kuma ake tuhumarsa da laifukan ta’addanci.