Labarai
An Gurfanar Da Wani Matashi A Gaban Kotu Bisa Zargin Kisan Dan Uwansa

An tura wani mutum mai suna Kingsley Bassey ranar Litinin a gidan yari na Kirikiri bisa zargin kashe kaninsa a lokacin da sha miyagun kwayoyi.
‘Yan sanda sun kama matashin mai shekaru 23, inda aka gurfanar da shi a gaban kotun Majistare da ke Yaba karkashin jagorancin Alkali Patrick Nwaka kan zargin kisan kai.
Dan sanda mai ganatar da kara, Thomas Nurudeen, ya shaida wa kotun cewa wanda ake kara ya aikata laifin ne a ranar 29 ga watan Mayun 2023 da misalin karfe 8:30 na safe a gida mai lamba 3, da ke kan titin kaji, a garin Meiran, na jihar Legas.
A cewar Nurudeen, laifin ya sabawa sashe na 222 kuma hukuncinsa ya dace a karkashin sashe na 223 na kundun dokar laifuka na jihar Legas 2015.
Laifin ya kara da cewa, “Kai Kingsley Bassey, a ranar 29 ga watan Mayu, 2023, da misalin karfe 8:30 na safe a gida mai lamba 3, da ke kan titin kaji, a garin Meiran, na jihar Legas.
An gurfanar da kai a wannan kotun Majistare ta Legas, kan zargin ka kashe wani yaro dan shekara shida ba bisa ka’ida ba (an sakaya sunansa) ta hanyar buga kansa a kasa.
“Ka aikata laifin da ya sabawa sashe na 222 da kuma hukunci a karkashin sashe na 223 na dokar laifuka ta jihar Legas 2015.”
Duk da haka, ba a karɓi roƙon wanda ake tuhuma ba.
Nurudeen ya roki kotun da ta ci gaba da tsare wanda ake kara har zuwa lokacin da za a bada shawarwarin shari’a daga sashin kula da kararrakin jama’a.
Alkalin kotun ya bayar da umarnin a tsare wanda ake tuhuma a gidan yari na Kirikiri .
Ya kuma dage sauraron karar har zuwa ranar 21 ga watan Agusta, 2023.