Featured
Masu zanga-zanga sun ɓalle ƙofar majalisar dokokin Najeriya
Masu zanga-zangar cire tallafin mai da ƙungiyoyar ƙwadago ta kasa (NLC) ke jagoranta sun ɓalle ƙofar shigar majalisar dokokin Najeriya.
Rahotanni sun bayyana cewa fusatattun masu zanga-zangar ta NLC da takwararta TUC sun ɓalla ƙofar shiga majalisar ne bayan taƙaddama da jami’an tsaro da ke gadin harabar majalisar.
Masu zanga zangar sun isa wurin ne bisa jagorancin shugaban NLC Joe Ajaero da takwaransa na TUC Festus Osifo, inda suka buƙaci jami’an tsaron su buɗe musu domin su shiga su gabatar da korafinsu, amma jami’an tsaro suka ki.
Daily Trust ta rawaito cewa hakan ce tasa ’yan kungiyar suka yi kukan kura suka karya kofar suka kutsa cikin harabar majalisar.
