Connect with us

Labarai

Tinubu Ya Rubutawa Majalisar Dattawa Wasikar Neman Tura Sojoji  Nijar

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya rubutawa majalisar dattawa wasika yana neman goyon bayanta ga tsoma bakin soja a kan mulkin soja a Jamhuriyar Nijar.

Ya kuma nemi goyon bayan majalisa kan katse wutar lantarki a kasar.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa jami’an tsaronsa sun hambarar da zababben shugaban kasar Nijar, Mohamed Bazoum.

A ranar Lahadin da ta gabata ne Tinubu, shugaban Najeriya kuma shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka, ya gana da wasu takwarorinsa na kungiyar ECOWAS.

Inda suka tattauna hanyoyin da suka dace don maido da mulkin dimokradiyya a Nijar.

Shugabannin kungiyar kasashen yammacin Afirka sun yi taro domin tattauna takunkumin da za a kakaba wa sojojin da suka hambarar da Bazoum a ranar 26 ga watan Yulin 2023.

Wasikar shugaban ta ce, “Yanayin siyasa a Nijar. Biyo bayan dambarwar siyasar jamhuriyar Nijar da ta kai ga hambarar da shugabanta, kungiyar ECOWAS karkashin jagorancina ta yi Allah wadai da juyin mulkin baki daya tare da kudurin neman dawo da gwamnatin da aka zaba bisa tafarkin dimokuradiyya da nufin dawo da zaman lafiya, ECOWAS ta kira taro ta fita tare da sanarwa.”

Shugaban ya ci gaba da neman goyon bayan, “amfanj sojoji da tura jami’ai don shiga tsakani na soji don tilasta barin tsarin mulkin soja a Nijar idan sun kafe.

“Rufewa da sanya ido kan iyakokin kasa Najeriya da Jamhuriyar Nijar da sake farfado da aikin iyakokin.

“Katse samar da wutar lantarki ga Jamhuriyar Nijar, tare da tara tallafin kasashen duniya don aiwatar da tanade-tanaden sanarwar kungiyar ECOWAS.”

“Hana gudanar da zirga-zirgar jiragen sama na kasuwanci da na musamman a ciki da wajen Jamhuriyar Nijar; Ya kara da cewa, tare kayayyakin da ke kan hanyar zuwa Nijar musamman daga Legas da tashoshin ruwa na gabas.

Tinubu ya kuma shaida wa majalisar dattawan cewa kasar na fara wayar da kan ‘yan Najeriya da ‘yan Nijar kan muhimmancin wadannan ayyuka, musamman ta kafafen sada zumunta.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet