Labarai
Gwamnatin Jihar Kano Ta Dakatar Da Shugabannin Asibitin UROLOGY

Gwamnatin Jihar Kano Ta Dakatar Da Shugabannin Asibitin UROLOGY
Gwamnatin jihar Kano karkashin Engr. Abba Kabir Yusuf, ta dakatar da Shugabanin Asibitin kula da masu ciwon yoyon fitsari na Abubakar Imam.
Gwamnatin ta dakadar da Dr. Atiku Adamu da Kuma Kabiru Ahmad, Wadanda ake zargin su da badakalar kudi da kuma kayan aiki.
Haka kuma Gwamnati tana zargin shugabanin da karya dokokin aiki.
Dakatarwar ta fito ne daga Hukumar Lura da asibitocin jihar Kano, ta bakin mai magana da yawun Hukumar, Hajiya Samira Ahmad.
KARAMTA WANNAN KUMA Gombe: NDLEA Ta Kama Wasu Mutane Bisa Zargin Safarar Miyagun Kwayoyi
Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA reshen jihar Gombe, a tsakanin watan Janairu zuwa Yuli, ta kama mutane akalla 214 da ake zargi da laifukan da suka shafi muggan kwayoyi.
Jami’an NDLEA sun kuma kama kilogaram 93.95 na tabar wiwi, da kilogaram 257.5Kg na sinadarin psychotropic da methamphetamine daga hannun wadanda ake zargin a cikin lokacin da ake bincike.