Labarai
N.9m: Wata Budurwa Ta Maka Saurayinta A Kotu Bisa Watsar Da Ita

Wani mutum mai suna Hassan Umar ya gurfana a gaban wata kotun majistare da ke Kano, bisa zarginsa da watsar da budurwar sa bayan ta kashe masa Naira 900,000.
Lauyan mai kara ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhumar ya yi ikirarin cewa yana kaunar wadda yake karewa da yarjejeniyar cewa za su yi aure.
Ya ce bayan wadda yake karewa ta kashe masa kudi, wanda ake zargin ya ki aurenta, sai ya jefar da ita ya daina zuwa wurinta.
Lokacin da aka karanta masa tuhume-tuhumen, wanda ake kara ya musanta aikata laifin.
Alkalin kotun, Salisu Hussaini, ya bukaci bangarorin biyu su kawo shaidunsu a zaman da za a yi na gaba.
Da take magana bayan zaman kotun, matar ta ce, “Ina shakkar bai yi min layya ba. Duk abin da ya tambaye ni na yi nan take. Na dafa masa abinci iri-iri, har da kaza, nama, har da raguna biyu. Na kashe sama da N900,000 a kansa. Amma daga nan ya fara nuna min kamar bai damu ba. Daga baya ya daina zuwa wurina.