Labarai
Juyin Mulki: Sheikh Bala Lau Ya Jagoranci Tawagar Malamai Zuwa Nijar

Wani babban malamin addinin musulunci kuma shugaban kungiyar Jama’atu Izalatu Bidi’ah wa Ikamatus Sunnah, da babbar kungiyar Salafiyya a Najeriya, ya isa jamhuriyar Nijar tare da sauran malaman addinin musulunci na Najeriya.
A wani bangare na kokarin diflomasiyya na maido da zaman lafiya a wannan kasa ta yammacin Afirka. Wakilinmu ya tabbatar da zuwan malaman a ranar Asabar din nan.
Jaridar PUNCH ta bayyana cewa Lau ne zai jagoranci tawagar malaman addinin musulunci bayan amincewar shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya baiwa malaman damad su shiga tsakani da tattaunawa da takwarorinsu na jamhuriyar Nijar.
Wata majiya da ke kusa da Shehin malamain ta ce tawagar za ta isa Nijar a ranar Asabar din nan.
Hotunan da wakilinmu ya rabawa manema labarai sun nuna cewa jami’an sojin Nijar sun tarbi malaman a ranar Asabar din nan da yamma.
Karin bayani kan matakai na gaba da malamai za su dauka har yanzu ba a kai ga bayyanawa ba.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa, a ranar Larabar da ta gabata ne shugaba Tinubu ya gana da shugabannin kungiyoyin addinin Islama daban-daban na kasar wadanda suka nemi amincewar sa kan su shiga tsakani da tattaunawa da takwarorinsu na Nijar.
Malaman da ke adawa da yakar sojojin Nijar, kamar yadda kungiyar ECOWAS ta yi barazanar, sun ce baya ga mummunar illar tashe-tashen hankulan da ke tattare da fadace-fadacen da ake shirin yi da makami, addininsu ya umarce su da kuma Alkur’ani da su fara neman sasantawa a irin wannan yanayi kafin neman yaki.
Sheikh Lau na kungiyar Izalla da Sheikh Abdurahman Ahmad na Ansar ud Deen, tare da shugabannin wasu kungiyoyi, sun yi wa manema labarai jawabi bayan ganawarsu da shugaba Tinubu.