Labarai
Gwamnan Jigawa Namadi Ya Kaddamar Da Rabon Kayan Abinci

Gwamna Mallam Umar Namadi na jihar Jigawa ya kaddamar da rabon shinkafa domin rage radadin tallafin man fetur ga ƴan kasa.
Gwamnan ya kaddamar da rabon kayayyakin ne a ranar Asabar a sakatariyar karamar hukumar Dutse.
Jaridar DAILY POST ta ruwaito cewa, gwamnatin jihar Jigawa ta amince da kudi sama da N134m domin siyan tireloli na shinkafa guda biyar domin karawa manyan motocin gwamnatin tarayya 5 domin rage tasirin cire tallafin man fetur.
Da yake jawabi a wajen taron, Gwamnan ya ce rabon shinkafar wani bangare ne na matakan da gwamnati ta dauka domin rage raɗaɗi.
“Kayan tallafin sun hada da buhunan shinkafa, da kuma tsabar kudi na nau’ukan masu kananan sana’o’i da za a zabo daga dukkan unguwanni da ke fadin kananan hukumomi 27 na jihar.
“Wannan mafari ne, saboda za a fara aiwatar da wasu manyan tsare-tsare nan ba da jimawa ba,” in ji shi.
Don haka ya roki jama’a da su yi hakuri da halin kuncin da kasar nan ke ciki, yana mai bayyana hakan a matsayin wani lamari na duniya.