Connect with us

Labarai

Kaduna: Kotun Sauraren Kararrakin Zabe Ta Kori Karar Da ‘Yan Takarar APC Suka Shigar

Kotun sauraren kararrakin zabe ta kasa da ke zamanta a jihar Kaduna ta yi watsi da karar da aka shigar kan wasu ‘yan majalisar wakilai biyu na jam’iyyar PDP.

A ranar Asabar din nan ne kotun ta yi watsi da karar da aka shigar kan David Umar Gurara mai wakiltar mazabar Kachia/Kagarko na tarayya da kuma Honarabul Bashir Shadow, mamba mai wakiltar mazabar Kauru ta tarayya.

‘Yan majalisar tarayyar guda biyu an sake zabar su karo na biyu a zaben ‘yan majalisar wakilai da hukumar zabe mai zaman kanta ta gudanar a ranar 25 ga Fabrairu, 2023.

‘Yan takarar jam’iyyar APC, Gabriel Haar Zock, da Mukhtar Zakari ne suka shigar da ‘yan jam’iyyar PDP biyu a gaban kotun.

A cikin karar da ya shigar, Gabriel ya yi zargin cewa ba a gudanar da zabe a rumfunan zabe 43 ba, yana mai neman kotun ta soke shaidar INEC da kuma umarnin sake gudanar da zabe.

Shi ma Mukhtar Zakari, ya shigar da karar Shadow bisa zarginsa da gabatar da takardar shedar makaranta ta jabu, ya kuma roki kotun da ta umurci hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta ba shi takardar shaidar cin zabe saboda ya zo na biyu a lokacin zaben.

Da yake yanke hukunci a cikin karar da Gabriel Haar Zock ya shigar, shugaban kotun, Mai shari’a H.H Kereng, wanda ya yanke hukunci a karar David Umar Gurara ya bayyana cewa mai shigar da karar ya kasa bayar da sahihan shaidun da za su tabbatar da karar sa. Ya yi watsi da bukatar gaba dayanta.

Haka kuma, yayin da yake yanke hukunci kan karar da Mukhtar Zakari ya shigar a kan Bashir Shadow, Mai shari’a Hon. Justice Abdu Maiwada Abubakar ya yi watsi da karar saboda rashin cancanta.

Daya daga cikin manyan lauyoyin wadanda ake karan guda biyu Kassai Jessy, ya ce kotun ta yi watsi da kararrakin da masu shigar da kara biyu suka shigar saboda rashin cancanta.

Jaridar PUNCH ta rawaito cewa Kotun ta yi kaurin suna wajen kin sanya tara ga wadanda suka shigar da kara saboda bata mata lokaci.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet