Labarai
Wani Hatsarin Mota Ya Yi Sanadin Rayuka Shida — FRSC

Hukumar kiyaye afkuwar hadura ta tarayya FRSC reshen jihar Osun, ta ce mutane shida ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin da ya afku a babbar hanyar Imesi-Ile a jihar.
Kwamandan shiyyar, Henry Benamesia, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Misis Agnes Ogungbemi, ta fitar a ranar Lahadin nan a Osogbo.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa Benamesia ta ce motoci biyu sun yi karo da juna ranar Asabar da misalin karfe 9:44 na dare sakamakon birki da ya dauke, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane shida.
Ya ce wata mota kirar (Red DAF) wacce ba ta da lamba, ta yi karo da wata babbar motar kasuwanci shudiyya a tsaunin Imesi -Ile tare da jikkatar mutane sakamakon gudu da ta ke yi.
“Muna da matattu biyar da ‘yan sandan Najeriya suka kai asibitin koyarwa na jami’ar Osun kafin isowar tawagar FRSC.
“Wanda ya mutu na karshe ya makale a karkashin motar kuma mun sami damar yin amfani da wata na’ura da aka kawo don cire gawar da ta makale daga daya daga cikin motocin,” in ji Benamesia.
A cewarsa, hatsarin ya rutsa da mutane 17 inda 11 suka tsira ba tare da jikkata ba yayin da wasu shida suka rasa rayukansu.
Ya kuma umarci masu amfani da hanyar da su tuka mota da nutsuwa domin gujewa afkuwar haduran kanya.
Benamesia, ta shawarci direbobi da su yi tuƙi cikin taka-tsan-tsan tare da tabbatar da cewa motocin nasu suna cikin yanayi mai kyau kafin su fara kowace tafiya. NAN