Labarai
Wasu Da Ake Zargin ‘Yan Bindiga Ne Sun Kashe Baturen ‘Yan Sanda

Rundunar ‘yan sandan jihar Ribas ta sha alwashin bin diddigi tare da gurfanar da wasu ‘yan bindiga da suka yi wa daya daga cikin jami’an ‘yan sandan shiyya, Bako Angbanshin kwanton bauna a unguwar Odumude da ke karamar hukumar Ahoada ta Gabas a jihar a daren ranar Juma’a.
Rundunar ‘yan sandan ta ce, Angbanshin ya jagoranci tawagar jami’an ‘yan sanda sun kai sumame a wasu maboyar ‘yan ta’adda a yankin, yayin da suke dawowa, wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne suka yi musu kwanton bauna.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Emeka Nwonyi, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Grace Iringe-Koko, ya fitar a safiyar ranar Asabar din nan kuma ya rabawa manema labarai.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa a daren Juma’a ne wani faifan bidiyo ya fito wanda ke nuna lokacin da ‘yan bindigar suka nuna gawarsa da aka yanka.
KARANTA WANNAN Hukumar EFCC Ta Cafke Wasu Da Ake Zargi Da Damfara Ta Intanet
Nwonyi ya bayyana cewa yayin da barayin suka far wa jami’an, mutanen Angbanshin sun ja baya bayan sun karar da harsashinsu.
Sanarwar ta kara da cewa marigayi DPO ya samu munanan raunuka, kuma ‘yan bindigar sun kama shi, wanda ya yi sanadin mutuwarsa.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “A wani mummunan lamari da ya faru a yammacin ranar 8 ga Satumbar, 2023, DPO na sashen Ahoda, SP Bako Angbashim, ya nuna jarumtaka a lokacin da yake kokarin yaki da miyagun ayyuka a yankin Odumude da ke karamar hukumar Ahoada ta Gabas a cikin jihar Ribas.
“SP Bako Angbashim, tare da tawagarsa da suka sadaukar da kansu, sun kai wani samame a wasu sansanonin masu aikata laifi a yankin. Wannan sumame ya kai ga bin sahun masu aikata laifuka daga maboyar da suka buya. Abin takaici, yayin da suke dawowa daga wannan sumame, wasu ’yan ta’adda da dama sai suka yi musu kwanton bauna, inda suka bude wuta kan jaruman jami’an.
“A cikin wannan hali da ake ciki, SP Bako Angbashim ya jajirce ya tsaya tsayin daka, yayin da mutanensa da suka karar da harsashi, sai suka ja da baya da dabara.
“Abin takaici, a yayin wannan al’amarin, SP Bako Angbashim ya samu munanan raunuka, kuma daya daga cikin masu ba da labarin shi ma ya samu rauni, a halin yanzu yana samun kulawar lafiya sakamakon harbin bindiga.”
Rundunar ‘yan sandan ta bayyana cewa an tuntubi jami’an sojin Najeriya domin neman agaji, amma ba su samu damar shiga cikin dajin ba saboda sanarwar ta bayyana a matsayin ‘yanayi mai tsananin duhu a cikin daji.
“Masu laifin sun kwace gawar SP Bako Angbashim, inda suka tilasta sauran jami’an su koma sansaninsu domin karfafa musu gwiwa. An yi kokarin cetowa tare da kwato gawar DPO, tare da neman taimako daga rundunar sojojin da ke FOB Base Etraco.
“Duk da haka, aikin ya zama kalubale saboda tsananin duhun da ke cikin daji,” in ji ‘yan sandan.
Yayin da yake jajantawa iyalan Angbashim, CP, ya sha alwashin gurfanar da wadanda suka aikata wannan aika aika a gaban kuliya.
Pingback: Gwamnatin Kano Za Ta Dawo Da Karbar Harajin Masu Adaidaita Sahu Kullum - KAKAKI HAUSA