Labarai
Biza: Dubai Ta Dage Haramcin Da Ta Sanyawa ‘Yan Najeriya

Hadaddiyar Daular Larabawa a ranar Litinin din nan ta dage haramcin bizar da ta sa wa ‘yan Najeriya na tsawon watanni.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kamfanin jiragen Etihad da na Emirates za su ci gaba da gudanar da zirga-zirgar jiragen zuwa Najeriya nan take.
Matakin ya biyo bayan tattaunawar da shugaban Kasar Najeriya, Bola Ahmad Tinubu, da takwaransa na Masarautar Mohamed bin Zayed Al Nahyan suka yi.
“Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa, Mohamed bin Zayed Al Nahyan, a ranar Litinin din nN a Abu Dhabi, sun kammala wata yarjejeniya mai cike da tarihi, wadda ta kai ga dakatar da dokar hana shigar ‘yan Najeriya nan take.
“Bugu da ƙari kuma, bisa wannan yarjejeniya mai cike da tarihi, kamfanonin jiragen saman Etihad da Emirates za su dawo da jadawalin tashi da saukar jiragen sama na shige da fice Najeriya nan take.
“Umarnin zai fara aiki ba tare da wani bata lokaci ba,” in ji mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale, a wata sanarwa da ya sanya wa hannu a ranar Litinin.