Labarai
‘Yan Sanda Sun Kama Mutane Uku Da Ake Zargi Da Hallaka Mataimakin Sanata

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta yi holan wasu maza uku da ake zargi da hannu a kisan Adeniyi Sanni, mataimaki na musamman ga Sanata Solomon Adeola wanda aka fi sani da Yayi.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas, Idowu Owohunwa ne ya bayyana kamen a ranar Litinin din nan yayin ganawa da manema labarai a shedikwatar rundunar da ke Ikeja, a jihar Legas.
Sanni ya mutu ne a ranar 5 ga watan Agusta lokacin da wasu mutane suka tare shi a wani shingen bincike a Ojodu Berger a kan hanyarsa ta zuwa gidansa da ke Legas.
Wadanda aka kama sun hadar da Fred Azeez Okuno, dan shekara 43 mazaunin Legas; da Lucky Idudu Michael, mai shekaru 33 daga jihar Delta; da Adedigba Segun, mai shekaru 26 daga Ibadan, a jihar Oyo.
“Ta hanyar zurfafa bincike da ayyukan kwakwaf wadanda suka karawa rundunar ‘yan sandan Legas kwarin gwiwa, mun yi nasarar cafke ‘yan fashi da makami.
“An kama mutane ukun da ake zargi da hannu a fashi da kisa kai tsaye da bindigogi uku ciki har da makamin da suka yi kisan,” in ji Legas CP.