Connect with us

Labarai

Gwamnatin Zamfara Ta Bada Da Umarnin Daukar Tsauraran Matakai Kan Masu Hakar Ma’adanai

Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara a ranar Asabar din nan ya bayar da umarnin hana ayyukan hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, ya kuma umarci jami’an tsaro da su dauki tsattsauran mataki kan masu keta haddi doka a jihar.

Tsawon shekaru, hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a jihar Zamfara na kara ruruta wutar ‘yan fashi da sauran miyagun ayyuka.

Gwamna Lawal, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya ce lokaci ya yi da za a kawo karshen wannan barna da kuma aiwatar da matakan kare lafiya da jin dadin jama’a.

Ya jaddada cewa an bai wa jami’an tsaro umarnin daukar tsattsauran mataki tare da harbe duk wanda aka samu yana aikin hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba.

Ya ce: “Wannan umarni ya zama dole don tabbatar da kariya da tsaron mutanen Zamfara da kuma hana masu aikata miyagun laifuka aikata irin wadannan ayyuka.

“Haka kuma wani mataki ne na gaggawa don baiwa Gwamnatin jiha damar kula da dukiyar jihar baki daya tare da dakile ayyukan da ke barazana ga rayuka da dukiyoyin jama’a.

“Babu shakka, hako ma’adinai ba bisa ka’ida ba na daya daga cikin aikin ’yan bindigar da suka addabi jihar Zamfara.

“Dole ne mu dauki matakin gaggawa, mai tsauri don dakile wannan barazanar”.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet