Connect with us

Labarai

NLC, Da TUC Sun Ayyana Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani Daga 3 Ga Watan Oktoba

Kungiyoyin Kwadago na Kasa NLC da TUC sun kuduri aniyar dakatar ayyuka a fadin kasar daga ranar 3 ga watan Oktoba, 2023, biyo bayan abin da kungiyar kwadago ta yi wa lakabi da gazawar gwamnatin tarayya.

Sun bayyana cewa gwamnati ta gaza wajen samun nasarar aiwatar da tsare-tsare na rage radadin da ‘yan Najeriya ke ciki bayan cire tallafin.

Jaridar PUNCH ta rawaito cewa shugaban NLC na kasa, Joe Ajaero, a yayin wani taron majalisar zartaswa ta kasa wanda aka gudanar a ranar Talatar nan ya shaidawa mambobin NEC cewa an gudanar da taro da jami’an TUC don tattaunawa kan hanyoyin da za a bi.

Ajaero ya yi nuni da cewa, an cimma matsaya kan cewa kungiyoyin biyu za su yi aiki tare domin bayyana matsayinsu ga gwamnati.

Wata majiya da ta halarci taron ta bayyana cewa tun da farko wasu daga cikin ‘yan kungiyar ta NLC sun nuna rashin amincewa da ci gaban kungiyar ta NLC da ke aiki tare da TUC.

“Da farko wasu mambobin ba sa son mu yi aiki da TUC amma har yanzu, ba mu da zabi. Gwamnati ba ta taka rawar gani ba. Don haka zai zama tabbataccen mataki a wannan karon.”

Jaridar Punch ta rawaito cewa wa’adin kwanaki 21 da kungiyar NLC ta bayar ya kare ne a makon jiya. Shugaban NLC na kasa, Joe Ajaero ya koka da cewa “babu daya daga cikin bukatun da aka gabatar a gaban gwamnatin tarayya da aka biya.”

Kungiyar ta fara yajin aikin gargadi na kwanaki biyu a fadin kasar a ranakun 5 da 6 ga watan Satumba domin nuna shirinta na shiga yajin aikin cikin wata guda.

Daga cikin abubuwan da NLC da TUC suke nema sun hadar da kyautatuwar albashi, aiwatar da ayyukan jin kai, cire haraji da alawus ga ma’aikatan gwamnati da kuma duba mafi karancin albashi.

A ranar 19 ga watan Yuni ne shugaban kasa Bola Tinubu ya kafa kwamitin gudanarwa na shugaban kasa da wasu kananan kwamitoci daban-daban domin tattauna tsarin da za a dauka a kan ayyukan jin kai.

Ko da yake Gwamnatin Tarayya ta yi alƙawarin sake fasalin tsarin haɗin gwiwa tare da ƙungiyoyin ma’aikata kan ayyukan jin daɗi, wa’adin makonni takwas da aka gindaya na kammala aikin ya ƙare a watan Agusta ba tare da ɗaukar wani mataki ba.

An bai wa kwamitocin wa’adin makonni takwas da su kammala aikinsu tare da gaggauta aiwatar da tsare-tsaren da za su dakile illar cire tallafin man fetur ga ‘yan Najeriya amma makonni bayan cikar wa’adin, kananan kwamitocin ba su yi taro ko aiwatar da ayyukansu ba, inda suka bar shugabannin kungiyar NLC da TUC ciki takaici.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet