Siyasa
An Bukaci ‘Yan Najeriya Da Su Tanadi Isasshen Abinci, Yayin Yajin Aikin NLC — Jam’iyyar LP

Jam’iyyar Labour ta bukaci magoya bayanta a duk fadin kasar nan da su cika gidajensu da kayayyakin abinci da suka dace gabanin yajin aikin da kungiyoyin kwadago ke shirin yi.
Jaridar KakakiHausa ta rawaito cewa kungiyar kwadago ta Kasa NLC, da kuma kungiyar ‘yan kasuwa, TUC, sun sanar da tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a ranar 3 ga watan Oktoba saboda gazawar gwamnati.
A wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba ta hannun sakataren yada labaranta Obiora Ifoh, jam’iyyar Labour ta kuma bayyana goyon bayanta ga yajin aikin da ake shirin yi.
A cewar jam’iyyar, gwamnatin shugaba Bola Tinubu ba ta damu da wahalar da al’umma ke ciki ba bayan cire tallafin man fetur.
Jam’iyyar ta koka da cewa yanayin tattalin arzikin kasar ya sa iyayen da suka kasa biya wa ‘ya’yansu kudaden makaranta sun daina zuwa.
Wani bangare na sanarwar ya kara da cewa Jam’iyyar LP ta bada cikakken goyon bayan kudurin kungiyar kwadago ta Kasa NLC, da kuma kungiyar ‘yan kasuwa, TUC, na fara yajin aikin wanda aka shirya farawa a ranar Talata 3 ga watan Oktoba.
Jam’iyyar Labour ta yi mamakin yadda gwamnati ke ikirarin cewa ta cire tallafin man fetur kuma yanzu haka tana samar da sama da Naira tiriliyan daya a kowane wata, amma duk da haka aka kasa magance bukatun ma’aikata.
A kullum ‘yan Najeriya na fuskantar tabarbarewar tattalin arziki inda hauhawar farashin kayayyaki ya kusan kashi 30 cikin 100, yayin da ake sayar da dala daya akan N1000, sannan kuma kudin shiga na kowane mutum ya ragu.
Iyalai da yawa suna cire yaransu daga makarantu saboda karin kudin makaranta, yayin da aikata laifuka ke karuwa kullum.