Labarai
Sashen Binciken Manyan Laifuka Za Su Karɓi Ragamar Binciken Zargin Zubawa Ministar Yawon Buɗe Ido Guba

Kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya, Haruna Garba, ya umurci sashin binciken manyan laifuka ta jihar da ta gaggauta karbe ragamar binciken da ke ofishin ‘yan sandan Mabushi.
A ci gaba da gudanar da bincike kan zargin saka gubar da aka yi wa ministar yawon bude ido Lola Ade-John, wadda ta yi sanadiyyar kwantar da ita a asibitin tarayya.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, ne ya bayyana hakan a ranar Asabar din nan a wata tattaunawa ta musamman da ta yi da wakilinmu ta wayar tarho.
SP Adeh ya bayyana cewa, “CP ya umarci rundunar ‘yan sanda ta Mabushi da ke binciken lamarin da su gaggauta mika shi ga sashin binciken manyan laifuka SCID.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa Ade-John mai shekaru 60, wadda shugaba Bola Tinubu ya nada a matsayin minista a watan Agusta, tana kwance a asibitin Abuja bayan da aka ce ta sha wata guba da ba a san asalinta ba, saboda ‘yan uwanta na fargabar cewa lokaci ya kure a kan kokarinsu na ceto rayuwarta.
An tattaro cewa an garzaya da ministar zuwa cibiyar kula da lafiya ta tarayya da ke Jabi, jim kadan bayan ta fara bayyanar da alamun rashin lafiya, kamar yadda majiyoyin ‘yan uwa da suka san halin da ta shiga suka bayyana. Ta shafe kwanaki biyar a wurin har zuwa safiyar Asabar, kamar yadda wakilinmu ya tattaro.
Ba a samu samun jami’an hukumar ta FMC ba saboda ba su amsa kiran waya da sakonnin tes daga wakilinmu ba.