Connect with us

Labarai

Bayan Kwato N27bn, Da $19m, EFCC Za Ta Binciki Tsofaffin Gwamnoni Da Ministoci

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta ce ta kwato kudaden da suka kai naira biliyan 27,184,357,524.52 da dala miliyan 19,084,419.33 daga cikin shari’o’i uku na halasta kudaden haram, yayin da ake ci gaba da kokarin kwato wasu haramtattun kudaden.

Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta ce nan ba da jimawa ba za ta fito fili, don yin bayani dalla-dalla kan binciken da ta ke yi kan wasu tsofaffin gwamnoni, da tsofaffin ministoci, da wasu jami’an gwamnati da dama a fadin tarayyar kasar nan, bayan samun koke da dama.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawar na ci gaba da gudanar da bincike a kan wasu manya-manyan badakaloli da suka shafi wasu jami’an ma’aikatar wutar lantarki ta tarayya da na ma’aikatar gona.

Kakakin hukumar ta EFCC, Dele Oyewale ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin da yake magana a madadin mukaddashin shugaban hukumar, Abdukarim Chukkol, yayin wata tattaunawa da manema labarai da wasu zababbun ‘yan jarida a Legas.

Oyewale ya ce hukumar ta kama wasu gidaje a babban birnin tarayya, Legas da kuma jihar Cross River wadanda kudaden da aka ware domin ayyukan wutar lantarki ne na Mambilla da Zungeru da aka karkatar ta hanyar wasu ma’aikatan ofishin canji.

“A laifuka daban-daban guda uku, hukumar ta kwato N27,184,357,524.52 da $19,084,419.33. Yayin da ake ci gaba da aiki, ayyukan hukumar suna ci gaba da tafiya daidai da aikin da aka ba mu yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen kawo karsen matsalar.

“An karbi koke-koke game da wasu jami’an gwamnati, wasu daga cikinsu tsofaffin gwamnoni, wasu tsofaffin ministoci, da wasu jami’an ma’aikatar, kuma ana ci gaba da bincike kan wadancan koke-koke; duk da haka, nan ba da jimawa ba za a bayyana cikakkun bayanai game da masu hannu da kuma binciken mu.

“Har ila yau, ana ci gaba da gudanar da bincike dangane da manyan zamba da suka shafi wasu jami’an ma’aikatar wutar lantarki da aikin gona ta tarayya; zamba a zahiri. Ana karkatar da kuɗin da aka ware don ayyukan wutar lantarki na Mambilla da Zungeru ta hanyar ma’aikatan Ofishin Canji kudi.

“A yanzu haka ana ci gaba da kwato gidaje da dama da aka saya da kudaden. Gidajen suna Abuja da Legas da kuma Cross River,” in ji Oyewale.

Jaridar PUNCH ta rawaito cewa, a watan Satumba ne hukumar EFCC ta yi wa tsohon ministan wutar lantarki, Olu Agunloye tambayoyi kan badakalar $6bn Build, Operate and Transfer.

A farkon watan Mayu ne dai Hukumar EFCC ta kama tsohon Ministan Wutar Lantarki, Sale Mamman, tare da tsare shi bisa zargin almundahanar N22bn.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet