Connect with us

Labarai

Neja: Jami’an Tsaro Sun Kama Wani Mutum Da Ake Zargi Da Satar Wasu Dawakai

Jami’an tsaro sun cafke wani mutum dan jihar Kaduna da ake zargin yana da hannu wajen satar dawakai guda biyu a Nijar.

Wanda ake zargin ya yi shirin jigilar dawakan da aka sace zuwa jihar Kaduna amma aka kama shi.

Rundunar ‘yan sandan jihar Neja, ta bakin kakakinta, Wasiu Abiodun, a ranar Alhamis din nan, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, wani Ahmed Aliyu na Zariya a jihar Kaduna ya sace dawakai mata guda biyu a wata gona a jihar Neja ya boye su a cikin wani daji kafin ya shirya da masu safara domin kai su zuwa Kaduna akan farashin N100,000.

“A ranar 4 ga watan Oktoba, da misalin karfe 14:30, an samu rahoton bacewar dawaki a wata gona a kauyen Chekungi ta Bida, a jihar Neja a ‘A’ Div Bida, da misalin karfe 21:10 na dare, a ranar 3 ga watan, an bace dawakai mata biyu a cikin gonar, inda aka ajiye dawakai kusan biyar.

“Masu karar sun yi zargin wani Ahmed Abubakar Aliyu na Zariya, a Kaduna wanda ke gonar kuma ya ziyarci gonar domin yin gyaran dawakan.

“Nan da nan aka kama wanda ake zargin, kuma a lokacin da ake masa tambayoyi, ya amsa laifin da ya aikata inda ya kwashe dawakan biyu zuwa wani daji da ke kusa da gonar, inda daga bisani ya dauki hayar mota daga wurin shakatawa domin ya kwashe dawakan zuwa Kaduna kan kudi N100,000.

“Bisa ikirari, an tuntubi direban motar ya jefar da dawakan a Mararaban-Jos, da ke Kaduna, yayin da aka shirya wata motar da za ta kai dawakin zuwa Bida,” in ji Abiodun.

Kakakin ya bayyana cewa wanda ake zargin yana tsare kuma ana gudanar da bincike kan lamarin.

“Za a gurfanar da shi a gaban kotu domin girbe abun da ya shuka nan da nan bayan an kammala bincike,” in ji shi.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet