Labarai
Kwamishinan ‘Yan Sanda Ya Bada Umurnin Korar Wani DPO Kan Zargin Almundahana

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Legas, Idowu Owohunwa, ya bayar da umarnin korar Baturen ‘yan sanda (DPO) da ke yankin Meiran a karamar hukumar Alimosho ta jihar nan take saboda abin da ‘yan sanda suka kira da rashin bin shugabanci da rashin bin doka da oda.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun ‘yan sanda a Legas, Benjamin Hundeyin ya fitar, baya ga DPO, an gano dukkan jami’an da ake zargi da laifin karbar wani dillalin waya, kuma a halin yanzu suna shedikwatar rundunar inda aka fara bincike.
Matakin ladabtar da ‘yan sandan ya biyo bayan rahoton da ake zargin jami’an ‘yan sanda daga ofishin ‘yan sanda na Meiran na karbar kudi N200,000 daga wani dillalin waya.
Rahotanni sun bayyana cewa jami’an sun tsare dillalin wayar da dan uwansa ne saboda rashin bayar da katin shaida ko kuma takardar shaidar mallakar wayar iphone da aka samu tare da dan uwansa.
Tashar talabijin ta Channels ta rawaito cewa, Rahotanni sun bayyana cewa an tsare su ne bisa zargin sata da fashi da makami har sai da suka tattauna kan sakinsu idan sun biya kudi N200,000 ga ‘yan sandan.