Featured
Gwamna Dauda Ya Bukaci Kantomomin Da Ya Nada Da Su Taimaka Wajen Kawar Da Rashin Tsaro

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya amince da nadin kantomomin riko da zasu shugabanci kananan hukumomi 14 na jihar.
Gwamnan ya kuma amince da nadin sakatarori da kansilolin sa ido na kananan hukumomin.
Gwamna Dauda Dare a wata sanarwa da babban mai taimaka masa na musamman Malam Sulaiman Idris ya fitar, ya ce an zabo wadanda aka nada cikin tsanaki bisa la’akari da nasarorin da aka samu a baya da kuma tarihin aikinsu na gwamnati sai aka nadasu.
Wadanda aka nada sun hada da Bashar Musa na karamar hukumar Anka, Sa’idu Danbala na Bakura, Isiyaka Ibrahim na Birnin-Magaji da Nasiru Muhammad na Bukkuyum.
Sauran sun hada da Nura Umar na Bungudu, Aminu Nuhu na Gummi, Yahaya Garba na Gusau, Kasimu Sani-Kaura na Kauran-Namoda da Yahaya Giwa na Maradun.
Sai Yusuf Sani-Bindin na Maru, Lukman Jafar na Talata-Mafara, Aliyu Adamu-Barmo mai wakiltar Tsafe, Junaidu Muhammad-Barade mai wakiltar Shinkafi da Aminu Atiku na Zurmi.
Sanarwar ta ce nadin na tsawon watanni shida ne kuma majalisar dokoki ta amince da nadin da aka yi.
Daga karshe gwamnan ya bukaci sabbin kantomomin rikon da aka nada da suyi amfani da kwarewarsu wajen ganin sun baiwa marada kunya, kuma su tabbatar sun bada gudunmawarsu wajen ganin an kawar da matsalaar tsaro da ta dade tana ciwa jihar tuwo a kwarya.