Labarai
NSCDC Ta Tabbatar Da Kama Wasu Da Ake Zargi Da Yunkurin Auren Jinsi A Gombe

Hukumar kula da kadarorin gwamnati da tsaron al’umma ta Kasa NSCDC ta ce ta kama akalla mutane 76 da ake zargi da yunkurin yin auren jinsi a Jihar Gombe.
Mai magana da yawun rundunar reshen jihar Gombe SC Buhari Sa’ad ne ya bayyana haka a ranar Lahadi ga manema labarai.
Ya ce sun samu nasarar kama matasan ne bayan sun samu bayanan sirri cewa suna shirin wani biki na zagayowar ranar haihuwa da kuma auren jinsi.
Sa’ad ya shaida wa manema labarai cewa cikin mutu 76 da ake zargi, 59 maza ne inda 21 daga cikinsu suka tabbatar da cewa su ‘yan luwadi ne sai kuma mata 17 wadanda aka kama a wurin.
Ya ce da zarar an kammala bincike za a gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu.
Jaridar Kano Time ta rawaito cewa Ba wannan ne karon farko da ake kama masu yunkurin auren jinsi ba a Nijeriya domin ko a watan Yulin bana sai da hukumar Hisbah ta Kano ta kama wasu da ake zargi da yukurin auren jinsi.
Haka ma a watan Agustan da ya gabata rundunar ‘yan sandan jihar Delta ta kama sama da mutum 100 wadanda ake zarginsu da shirin na auren jinsi.