Connect with us

Featured

Ya Kamata Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakin Gaggawa Kan Tsadar Rayuwa Da Talakawa Ke Ciki – Aminu Rabi’u Ali

Ya kamata gwamnatin tarayya ta yi gaggawar daukar mataki domin dakile kuncin rayuwa da al’ummar kasa suka tsinci kan su a ciki biyo bayan tashin dala da kuma cire tallafin man fetur.

Shugaban kamfanin Biz Classics Nig Ltd, Alhaji Aminu Rabi’u Ali ne ya bayyana hakan ga manema labarai a jiya Talata, inda ya alakanta tsadar rayuwar da tashin dala da kuma cire tallafin man ferur, wanda ya zama dole mahukunta su yi duba kan lamarin.

“Tashin dala da cire tallafin man fetur sun yi matukar taimakawa wajen tsadar rayuwar da ake ciki a yanzu, kuma idan aka cigaba da kasancewa cikin irin wannan mawuyacin hali dole a kasa kawo karshen harkar tsaro duk da kokarin da ake yi, domin idan har mutum zai iya kwana da yunwa dole ta’addanci zai ta’azzara saboda rashin mafita”, cewar Alh Aminu Rabi’u Ali.

Aminu Rabi’u ya shawarci gwamnati da ta waiwayi ‘yan kasuwa ta hanyar samar musu da dalar da za su iya yin kasuwanci, wanda yin hakan zai taimaka matuka wajen rage tsadar kayayyaki.

Ya kuma bayyana ra’ayinsa game da tallafin da gwamnati take shirin baiwa ‘yan kasa, inda yake ganin hakan ba ita ce mafitar matsalolin tsadar rayuwa da kasar ke ciki ba, ya ce maimakon hakan gara a saka tallafi a harkar shigo da kayan abinci tunda an cire tallafin man fetur har sai lokacin da abinci ya wadatu ta yadda mai karamin karfi zai iya mallakar kayan abinci cikin sauki, idan ya so daga baya gwamnati sai ta duba idan da yiwuwar cigaba da tsarin saka tallafin shigo da kayan abinci.

Share this:
Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet