Featured
Da Dumi-Dumi: NLC Da TUC Sun Ayyana Yajin Aikin Gama Gari A Fadin Kasa

Kungiyar Kwadago ta Kasa NLC ta ayyana yajin aikin sai baba ta gani a fadin kasar nan baki daya.
NLC ta bayyana cewa yajin aikin zai fara daga ranar Talata, 14 ga watan Nuwamba, 2023.
Kungiyoyin Kwadago na NLC da TUC ne suka bayyana hakan bayan wani taron gaggawa da suka yi ranar Talatar nan a Abuja.
Idan za a iya tunawa, kungiyar kwadago ta yi barazanar shiga yajin aiki saboda harin da aka kaiwa shugaban NLC, Joe Ajaero, a jihar Imo a makon da ya gabata.