Featured
Gwamnatin Kano Ta Amince Da Sama Da Naira Biliyan 40 Don Gudanar Da Wasu Ayyuka

Majalisar zartaswar jihar Kano ta amince da sakin N40,353,117,070 domin gudanar da ayyuka daban-daban a jihar a taronta karo na 8.
Jaridar SOLACEBASE ta rawaito cewa Majalisar ta amince da bayar da Naira miliyan 15,974,357,203 ga ma’aikatar ayyuka da gidaje ta jiha domin gina hanyar karkashin kasa ta Dan Agundi da kuma gadar sama yayin da N14,455,507,265 na ginin Tal’udu Interchange Clover Leaf Flyover.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida Baba Halilu Dantiye ya fitar a daren ranar Litinin.
“Majalisar ta amince da sakin Naira 3,360,084,380 ga ma’aikatar ayyuka da gidaje domin sake duba farashin gina magudanan ruwa da aka rufe a bakin kogin Jakara-Kwarin Gogau, yayin da aka amince da N1,579,755,966 domin gina hanyar Kofar Waika zuwa Unguwar Dabai zuwa Yan Kuje Western bypass a karamar hukumar Gwale, “in ji sanarwar.
Hakazalika an baiwa ma’aikatar ayyuka da gidaje kudi N1,350,460,874 don gina hanyar Unguwa Uku ‘Yan Awaki-Limawa a karamar hukumar Tarauni, yayin da aka amince da N820, 262,071 don kammala titin Kanye-Kabo -Dugabau a cikin karamar hukumar Kabo.
Daga cikin kudaden da aka baiwa ma’aikatar ayyuka da gidaje domin gudanar da ayyuka daban-daban sun hada da naira biliyan 802,695,617 domin kammalawa da kuma hada aikin titin Kofar Dawanau-Dandinshe-Kwanar Madugu titin ll, N458,443,067 domin sake bayar da kwangilar gina simintin inganta gadojin masu tafiya a kafa a wurare daban-daban a fadin jihar, yayin da aka amince da Naira 420,000,000 don gyara fitulun manyan tituna domin masu ababen hawa.
Majalisar ta kuma amince da sakin N200,537,271 ga ma’aikatar ayyuka da gidaje domin biyan wasu makudan kudade dangane da kwangilar gyaran hanyar Kwanar Kwankwaso da ke karamar hukumar Madobi, da kuma N107,658,975 na ayyukan gyara a Cibiyar gyaran hali ta Kiru, dake karamar hukumar Kiru.
Majalisar zartaswar ta amince da sakin kudade ga ma’aikatar lafiya ta jihar da suka hada da N53,654,223 don siyan kayayyaki da magunguna da ake bukata na watan Oktoba 2023 don baiwa cibiyoyin kiwon lafiyar jama’a damar kula da Hatsari da Gaggawa, Kula da Mata da Yara kyauta a jihar, da N40,820,564 domin biyan magunguna da dakin gwaje-gwaje da kayan aiki da aka kai asibitin yara na Hasiya Bayero da naira miliyan 37,005,000 domin daidaitawa manufar gwamnatin jihar wajen wayar da kai kan rigakafin cutar mashako zagaye 3 a kananan hukumomi 22.
Majalisar ta amince da kudi naira miliyan 56,763,475 ga ma’aikatar ilimi ta jiha domin sake gina wani babban dakin taro da ya kone a kwalejin koyon addinin musulunci da shari’a ta Aminu Kano.
Majalisar ta yi nazari tare da amincewa da kwarya-kwaryar kasafin kudi na 2023 na biyu na gyare-gyare na N24,000,000,000 wanda ya hada da kashe kudi na yau da kullun na N4,000,000,000 da kashe babban kudi na N20,000,000,000: don haka ta amince da kasafin, N2023.