Connect with us

Featured

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Wa Da Amurka Martani Kan Barazanar Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta yi Allah wadai da gargadin tafiye-tafiyen da Amurka ta yi wa ‘yan kasarta da ke Najeriya, tana mai cewa irin wannan shawarar na iya haifar da firgici mara amfani da kuma illata tattalin arziki.

A ranar 3 ga watan Nuwamba, Amurka ta gargadi ‘yan kasarta a Najeriya game da “babbar barazana” a manyan otal-otal a cikin “manyan garuruwa” na Najeriya.

Shawarar, ta ce hukumomin tsaron Najeriya na kokarin dakile wannan barazana.

Da yake jawabi a wani taron tattaunawa da manema labarai a Abuja ranar Litinin, Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Idris, ya ce irin wannan shawarwarin zai kawo cikas ga kokarin da gwamnati ke yi na jawo masu zuba jari zuwa Najeriya.

Ya ce a ko da yaushe gwamnati tana ba da fifiko kan tsaro da jin dadin duk masu ziyartar Najeriya.

Mun aiwatar da tsauraran matakan tsaro a matakin tarayya da jihohi don tabbatar da tsaron masu yawon bude ido da kuma bakin kasashen waje.

Wadannan matakan sun hada da tattara bayanan sirri mai tsanani, saye da tura karin hanyoyin sadarwa, horo da horar da ma’aikata, hadin gwiwa da hukumomin tabbatar da bin doka da oda na kasa da kasa, da sauransu, don kiyaye tsaro, in ji shi.

Dangane da batun cire tallafin man fetir, Idris ya ce gwamnati mai ci ta samar da wasu abubuwan more rayuwa a takaice, matsakaita da kuma masu dogon zango don taimakawa wajen dakile illolin cire tallafin.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet