Featured
Gwamnan Zamfara Ya Tabbatar Da Samun Nasara A Yaki Da Ake Yi Da ‘Yan Bindiga A Jihar

Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya ce gwamnatinsa na ci gaba da samun nasara a yakin da ake yi da ‘yan bindiga a jihar.
Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Laraba, inda ya ce rukunin farko na rundunar kare jama’a (CPG), da aka dauka daga dukkan kananan hukumomin jihar 14, za a tura su sansanin horo nan da mako guda.
Jawabin nasa na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar.
Sanarwar ta ce gwamna Lawal ya karbi wata takardar daga zauren bada horo a gidan gwamnati da ke Gusau, babban birnin jihar.
A cewar sanarwar, kwamitin karkashin jagorancin Alhaji Bello Umar Karakkai tsohon shugaban ma’aikata na jihar Zamfara ne ya gabatar da takardar.
Gwamna Lawal, a lokacin da yake jawabi a yayin gabatar da takarda kan rahoton kwamitin horar da jami’an ya yabawa kwamitin bisa kwazon da suka yi na nazarin rahoton tare da gabatar da matsayin gwamnati kan batutuwa daban-daban da shawarwarin da aka gabatar a cikin rahoton.
Sanarwar ta kara da cewa, “Wannan ya yi daidai da yunkurin gwamnatin jihar Zamfara na magance matsaloli daban-daban da suka shafi tattalin arziki da tsaro a fadin jihar.