Featured
Matsalar Tsaro: Gwamna Abdullahi Sule Ya Yi Wata Ganawa Da Fulani A Nasarawa

Gwamna Abdullahi Sule na Nasarawa, ya gana da shugabannin kungiyar al’adun Fulani ta Miyetti Allah Kautal Hore, domin tattaunawa da kuma doba yadda za a magance matsalolin tsaro da ake fama da su a jihar.
Taron wanda ya gudana a gidan shugaban kungiyar na kasa Alhaji Abdullahi Bello Bodejo ya mayar da hankali ne kan neman goyon bayan kungiyar wajen yakar al’amuran da suka shafi garkuwa da mutane, fashi da makami, da sauran miyagun laifuka a jihar.
Sule ya jaddada bukatar hada kai da kungiyar da sauran kungiyoyin Fulani a jihar, don ganin yadda ake yawan samun wasu ’yan kabilar Fulani wajen kai hare-hare daban-daban.
Ya ce wasu al’amura da dama na faruwa ne daga mutanen waje da suka shigo cikin jihar, suna haddasa barna.
Gwamnan ya bukaci ‘yan banga na kungiyar Fulani da su taimaka wa jami’an tsaro wajen ganowa tare da dakile hare-haren da wasu mutane daga waje jihar suke kai wa.
Duk lokacin da aka yi garkuwa da mutane sai kaga an samu fulani da hannu a ciki, don haka ne na ga ya dace in tsaya a nan in yi magana da shugabannin Fulani kan bukatar ganin wasu batagari ba su shigo cikin jiharmu don yin ta’addanci ba.
Al’ummar Fulani a jihar Nasarawa masu son zaman lafiya ne, don haka ya kamata mu yi duk mai yiwuwa don ganin cewa wasu ba su shigo cikin jiharmu don aiwatar da miyagun ayyuka ba.