Featured
Haaland Ya Samu Rauni Yayin Buga Wasan Sada Zumunta

Dan kwallon kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Erling Haaland ya samu rauni kafarsa yayin da yake buga wani wasan sada zumunta da kasarsa ta Norway ta buga.
Mai horas da ‘yan wasan kwallon kafa ta Manchester City da magoya bayan ba su ji dadin wannan labarin jin raunin dan wasansu Haaland ba, Haaland wanda ya jefa kwallaye 17 a wasannin 18 da ya buga a bana.
Likitan tawagar kasar Norway Ola Sand ya bayyana cewar Haaland ya ji rauni a daidai inda ya yi fama jinya a kwanakin baya.
Manchester City dai zata kara da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool a kwanaki 9 masu zuwa a gasar Firimiya Lig ta kasar Ingila.