Featured
Adamawa: Rundunar ƴan sanda ta kama tsoho mai shekaru 53 da lalata yarinya mai taɓin hankali

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta kama wani mutum mai shekaru 53 mai suna Usman Ahmadu, bisa zarginsa da cin zarafin wata ƙaramar yarinya mai taɓin hankali.
Usman Ahmadu, wanda aka ce ya fito daga Maidugurin jihar Borno, yana zaune ne a matsayin dan gudun hijira, a unguwar Saminaka a karamar hukumar Yola ta Arewa.
Rundunar ‘yan sandan jihar tace, Usman Ahmadu ya amsa laifin yin lalata da yarinyar har sau hudu, tun daga shekarar 2021.
Sanarwar da rundunar ‘yan sandan jihar ta fitar wacce ta bayyana lamarin, ta ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Afolabi Babatola, ya bayar da umarnin gudanar da bincike mai zurfi tare da gurfanar da shi gaban kuliya.