Featured
Kotu Ta Sake Ɗage Shari’ar Emefiele Zuwa Janairun Sabuwar Shekara

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, ta ɗage shari’ar da ake yi wa tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), zuwa watan Janairun 2024.
Hakan zai sa ya ci gaba da zama a gidan yari har sai ya cika ka’idar belinsa ta kudi Naira miliyan 300.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ce, ta gurfanar da Emefiele bisa zarginsa da laifuka shida, ciki har da zargin badakalar kudi Naira biliyan 1.6 da kuma mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.
Sai dai tsohon gwamnan babban bankin ya musanta zargin.
Yanzu kotun ta ayyana 18 ga watan Janairun 2024 domin sake zama kan shari’ar.