Featured
Shugaba Tinubu zai yi balaguro a ranar Laraba zuwa ƙasar Dubai

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, zai yi tafiya a ranar Laraba zuwa birnin Dubai na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa domin halartar taron sauyin yanayi na COP28.
Wata sanarwa da ta fito daga hannun mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale, a yau Talata, ta ce Tinubu zai gabatar da jawabi a taron wanda zai gudana tsakanin ranakun 1 da 2 ga watan Disamba.
Bayanin da shugaba Tinubu zai gabatar lokacin taron zai mayar da hankali ne kan matsayar Najeriya game da sauyin yanayi, musamman abin da ya shafi amfani da makamashi maras gurɓata muhalli da kuma samar da kuɗi kan ayyukan daƙile ɗumamar yanayi.
Ana sa ran Tinubun zai yi amfani da damar wajen neman ƙasashen da suka ci gaba da su ƙara tallafa wa ƙasashe masu tasowa wajen yaƙi da sauyin yanayi.