Featured
Kano: Kotun Ƙoli Ta Kammala Sauraron Ƙarar Zaɓe, Za Ta Sanar Da Ranar Yanke Hukunci

A yau Alhamis 21, ga watan Disambar 2023, Kotun kolin Nijeriya da ke Abuja ta fara sauraren karar zaben gwamnan Kano da Gwamnan Kano Abba Kabiru Yusuf da Jam’iyyar NNPP da INEC suka shigar gabanta.
Ma su shigar da karar sunan kalubalantar hukuncin kotun sauraren karar zaben gwamnan Kano da Kotun daukaka kara da su suka ayyana dan takarar Jam’iyyar APC, Dr. Nasiru Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Kano.
A zaman na yau, tunda farko Kotun ta ce, ba ta da lokacin sauraren ƙarar NNPP da Abba da INEC da suka shigar gabanta har guda tara (9), sai dai su zaɓi guda ɗaya acikin tara.
Daga bisani kotun ta ba masu ƙara da wanɗanda ake ƙara minti 10 kowane bangare ya faɗi matsayarsa. Lauyoyin APC da NNPP duka sun gabatar da jawabansu a gaban kotu.
A nasa jawabin Lauyan INEC, ya gabatar da bayyanai kan tanadin da dokar zaɓe ta yi kan kuri’un zaɓe marasa satamfi da sa-hannu da kwanan wata.
Yayin zaman shari’ar na yau Kotu ta gamsu takardun shari’a na kotun ɗaukaka ƙara na farko cewa kuskure ne, ta kuma karɓi takardu na biyun bayan kotun ta gyara kuskuren da ke jiki.
Cikin tambayoyin da Kotu ta yi wa Lauyan hukumar zabe ta INEC ta tambaye shi shin ko waɗannan ƙuri’un zaɓen naku ne (Marasa satamfi da sa-hannu da kwanan wata)? Sai Lauyan INEC ya amsa da Eh ƙuri’unmu ne (bana bogi bane).
Daga bisani Kotu ta yi ƙarin haske kan batun satar ƙuri’un zaɓe a Nijeriya, wanda ta ce wajibi ne doka ta yi aiki don magance matsalar ba a iya Kano kaɗai ba a duk faɗin Nijeriya saboda wajibi ne kiyaye doka da oda.
A karshe Kotun ta kammala sauraron ƙarar, ta kuma ce za ta sanar da ranar yanke hukunci kan shari’ar.