Featured
Kotun Ƙoli Ta Tabbatar Da Nasarar Abba Kabir Yusuf

Kotun Ƙoli ta tabbatar wa da Gwamnan jihar Kano Injijiya Abba kabir yusif kujerarsa, inda ta soke nasarar da APC ta samu a kotunan kasa.
Kotun ta tabbatar da nasarar Abba ne bayan da ta dawo masa da kuri’un sa, sama da dubu 165.
Kuma hukuncin kotun kolin ya kawo karshen takaddamar a yau jumu’a, inda take ci-gaba da karanta hukunci akan sauran shari’un gwamnonin.