Featured
Gwamnatin Kano Za Ta Kashe Maƙudan Kuɗaɗe A Fannin ilimi

Gwamnatin jihar Kano ta yi alkawarin kashe makudan kudade a fannin ilimi domin biyan bukatun daliban jihar.
Jaridar KANO FOCUS ta ruwaito kwamishinan ilimi na jihar Alhaji Umar Haruna Doguwa ya yi wannan alkawarin ne a yayin wani taron tunawa da ranar ilimi ta duniya ta 2024, wanda aka gudanar a Kano.
A cewarsa, gwamnatin jihar karkashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf, ta ware kashi 29.7% na kasafin kudinta na shekarar 2024 ga ilimi, a wani bangare na kokarin farfado da fannin.
Ya ce, ayyukan da aka yi a fannin sun hada da, gyaran manyan motocin bas guda 60 don daukar dalibai mata, da kuma amincewa da Naira miliyan 740 don biyan kudaden jarrabawa, ga dalibai marasa galihu.
Umar Doguwa ya kara da cewa, jihar Kano ta shiga shirin Majalisar Dinkin Duniya na gwajin makarantun lafiya, inda a kowace shiyya ta ke da makarantu 48 maza da mata, baya ga horarwa da daukar karin malamai.
A nasa jawabin, sakataren zartarwa na hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar Kano (SUBEB), Alhaji Yusuf Kabir ya ci gaba da cewa, ilimi yana karfafar Dalibai a matsayin wakilan zaman lafiya, kuma makami ne mai karfi da zai canza rayuwar al’umma.