Featured
Abduljabbar Kabara Ya Nesanta Kansa Daga Masu Yunƙurin Ɗaukaka Ƙara Akan Hukuncin Da Aka Yanke Masa

Sheikh Abduljabbar Sheikh Nasiru Kabara, ya nesanta kan sa da mutanen da suke yunkurin daukaka kara a kan hukuncin da aka yanke masa a baya.
Abduljabbar ya bayyana hakan ne ta cikin wata takarda da ya rubuta mai kwanan wata 07 02 2024, aka aikewa manema labarai.
Abduljabbar Sheikh Nasir Kabara ya bayyana cewar bashi da wata alaka da mutanen da suke bayyana kansu a matsayin almajiransa.
Ya kuma bayyana cewar wannan yunkurin da masu niyyar daukaka karar suke yi ba da yawunsa suke yi ba.
Idan dai ba’a manta ba babbar kotun shari’ar muslinci ta kofar kudu ce dai ta yanke hukuncin kisa akan malamin sakamakon samunsa da laifin batanci ga Annabi S.A.W, tun a baya.
Majiyarmu ta rawaito cewa a makon da zamu shiga ne babbar kotun jaha za ta fara sauraron bangarorin da suka shigar da karar da kuma bangaren gwamnati.