Featured
Kano: Gobara Ta Laƙume Miliyoyin Naira A Kasuwar Ƴan Katako

Sama da shaguna 50 ne suka kone kurmus tare salwantar dukiyar miliyoyin Naira a wata gobara da ta tashi a kasuwar ’yan Katako da ke unguwar Rijiyar Lemu a ƙaramar hukumar Fagge ta Jjhar Kano.
Shugaban kasuwar, Mamuda Abdullahi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana cewa gobarar ta tashi ne da misalin karfe 1 na safiyar yau Litinin.
Ya ce shagunan da gobarar ta shafa na da katako, injin feshi, kujeru, da sauran kayan aikin kafinta a cikin su.
Sai dai ya yaba wa jami’an hukumar kashe gobara ta jihar, bisa kai dauki a kan lokaci da suka yi zuwa kasuwar.