Connect with us

Featured

Ƙididdiga ta nuna cewar a jihar Kano ne aka fi samun rahoton cin zarafi

An bukaci ‘yan jaridau dasu rika bin diddigin labarin da ya shafi cin zarafi, ba yada shi kadai a farko ba.

Kwamaret Isiyaku Ahmad ne ya bukaci hakan yayin wani taron baiwa ‘yan jarida horon wuni guda da cibiyar Stalion Time ta shirya ranar Laraba a Kano.

Kwamaret Isiyaku Ahmad, wanda shi ne shugaban Stalion Time ya ce an shirya taron ne domin yi wa ‘yan jaridu bitar yadda za su rika bibiya don tabbatar da an bi wa wanda aka ci zarafi hakkinsa ta kowace hanya.

Ya ce kididdiga ta nuna cewa a Kano aka fi cin zarafi, don haka ne ma suka zo jihar domin bada horon yadda za a rika bibiyar rahoton cin zarafi har sai an yi hukunci, kuma a guji yada kalamai ko rubuta kalaman da basu dace ba.

Da take jawabi yayin bada horon Farfesa Aisha Abdul Isma’il daga jami’ar Bayero ta ce cin zarafin jinsi abu ne da ya ke bukatar wayar da kai, don a fahimci kene cin zarafin domin ba iya mata ake cin zarafi ba ko kananan yara har ma da maza.

Farfesa Aisha Isma’il wadda ta gabatar da makala a wajen bitar mai taken kare hakkin mutanen da aka ci zarafi, ta ce ‘yan jarida na da gudunmawar da za su bayar wajen tabbatar da labari da kuma ganin anyi hukuncin da ya dace ta hanyar bin diddigin abun da ya faru har zuwa karshe.

Wakilinmu Nura Ahmad Hassan ya yin zantawarsa da wasu ‘yan jaridu da suka halarci taron bitar sun bayyana wa Kakaki24 cewa, sun karu matuka da wannan bitar kuma za su yi kokarin dabbaka abun da suka koya a aikace.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet