Connect with us

Featured

Tinubu Ya Bada Umarnin Bude Iyakokin Najeriya Da Nijar Nan Take

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya bai wa hukumomi umarnin bode iyakokin kasar ta kasa da sama da Jamhuriyar Nijar, tare da cire duk wasu takunkuman karya tattalin arzikin da aka dorawa kasar ba tare da bata lokaci ba.

Wannan umarni ya biyo bayan matsayin da kungiyar ECOWAS ta dauka a taron da shugabannin kasashen yankin suka gudanar a ranar 24 ga watan Fabarairun da ya gabata.

Kungiyar ECOWAS ta amince da cirewa kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso da kuma Guinea takunkumin da aka dora musu sakamakon juyin mulkin sojoji da aka samu a cikin su.

Sanarwar da mai magana da yawun shugaban Kasar Ajuri Ngelale ya rattabawa hannu, ta bayyana cewar shugaba Tinubu ya bada umarnin bude iyakokin kasa da na sama da kuma kawar da dokar hana shawagin jiragen saman ‘yan kasuwa tsakanin Najeriya da Nijar.

Umarnin shugaban ya kuma kunshi bude asusun ajiyar kudaden Nijar da kuma ci gaba da gudanar da huldar kasuwanci tare da bai wa kasar wutar lantarki.

Ngelale ya kuma ce wannan umarni na shugaba Tinubu ya kuma kunshi bude asusun ajiyar Jamhuriyar Nijar da hukumomin kasar dake bankunan kasuwanci tare da dawo da kasar cikin hukumomin da ake hada hadar kudade daban daban irin su EBID da BOAD.

Umarnin ya kuma kunshi bai wa jami’an gwamnatin Nijar damar tafiye tafiye tare da iyalansu.

Mai magana da yawun shugaban ya kuma bayyana cewar wannan umarni ya shafi hukumomin kasar Guinea.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet