Connect with us

Featured

‘Yan Bindigar Da Suka Sace Daliban Kaduna Sun Bukaci Kudin Fansa Cikin Kwana 20

Ƴan bindigar da suka yi garkuwa da ɗalibai 287 a wata makaranta a da ke jihar Kaduna makon da ya gabata, sun bukaci a ba su Naira biliyan ɗaya, kwatankwacin dala 620,432 a matsayin kuɗin fansa.

Kansilan yankin kuma mai magana da yawun iyalan wadanda aka yi garkuwa da ‘ya’yan su Jibril Aminu ne ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

A ranar 7 ga watan Maris din nan ne aka sace yara ƴan makaranta da ma wasu manyan ɗalibai da kuma wasu ma’aikatan makarantar a garin Kuriga da ke jihar Kaduna a arewa maso yammacin Nijeriya, a karon farko da aka yi garkuwa da mutane da dama irin haka tun shekara ta 2021.

Kansilan, Jubril Aminu, ya ce masu garkuwan sun kira shi ta wayar tarho ranar Talata, “Sun buƙaci a biya su jimillar naira biliyan ɗaya a matsayin kudin fansa ga ɗaukacin ɗalibai da ma’aikatan makarantar,” in ji Aminu.

“Sun ba da wa’adin biyan kudin fansar nan da kwanaki 20, daga ranar da aka yi garkuwa da su, sun ce za su kashe dukkan ɗaliban da ma’aikata idan har ba a biya kuɗin fansar ba.”

Shi ma Idris Ibrahim, wani zaɓaɓɓen jami’i a karamar hukumar Kuriga, ya tabbatar da batun bukatar kudin fansar da adadin kudin.

“E, masu garkuwa da mutane sun kira al’ummar ta lambar Jubril Aminu, suka kuma gabatar da bukatar,” in ji shi.

Ibrahim ya shaida wa Reuters cewa, “Sun kira ne daga wata ɓoyayyiyar lamba amma hukumomi na aiki don gano lambar.”

Ya ƙara da cewa jami’an tsaro na daukar ƙwararan matakai domin ganin an sako daliban.

Reuters ta ruwaito cewa Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna Mista Samuel Aruwan, bai amsa saƙon da ta aika masa ta son jin ta bakinsa game da buƙatar masu garkuwa da mutane ba.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet