Featured
Rundunar ‘Yan Sanda Ta Fara Aikin Ceto Shugaban Jam’iyyar PDP Da Aka Sace
Rundunar ‘yan sandan jihar Edo, a ranar Asabar, ta fara aikin ceto bayan sace shugaban jam’iyyar PDP a jihar, Tony Aziegbemi.
A ranar Juma’a ne wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da Aziegbemi jim kadan bayan wata ganawa da gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, a gidan gwamnati da ke birnin Benin.
Bayan tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ta fitar, gwamnatin jihar Edo ta ce tana hada kai da jami’an tsaro don ganin an samu ‘yanto shi.
Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a jihar, Chidi Nwabuzor, ya yi kira ga mazauna Edo da su baiwa ‘yan sanda bayanan da za su kai ga ceto Shugaban PDP a kan lokaci.
Ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Funsho Adegboye ya kafu samu rahoton faruwar lamarin.