Featured
Iyayen ‘Yan Mata Daliban Jami’ar Gusau Da Aka Sace Sun Musanta Batun Sakin ‘Ya’yansu

Iyayen ‘yan matan da aka sace a Jami’ar Tarayya ta Gusau a Jihar Zamfara, sun ce ba su da labarin sakin ’ya’yansu a hukumance.
Wasu Kafafen sadarwa musamman na intanet suka ruwaito cewa an saki sauran ‘yan mata guda tara da suka rage a hannun ‘yan bindigar.
A watan Satumbar bara ne dai wasu ‘yan bindiga suka kai hari gidajen ‘yan matan da ke daura da jami’ar a Unguwar Sabon Gida a birnin Gusau, kuma suka yi garkuwa da Daliban.
Mahaifin ɗaya daga cikin ‘yan matan, Dokta Ibrahim Mai Unguwa ya bayyana wa Jaridar Aminiya ta wayar tarho cewa shi dai har yanzu a kafafen sada zumunta yake ganin labarin an saki ‘ya’yan nasu, har ma an damka su ga hukumomin tsaro, amma shi babu Wanda ya kira shi kan an saki yaran.
Dokta mai Unguwa ya ce zai fi kowa farin ciki idan ta tabbata an saki yaran, kuma yana rokon Allah Ya tabbatar da sakin ‘ya’yan nasu.
Shi ma dai kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, Yazid Abubakar ya ce, ba su samu labarin sakin yaran ba.