Featured
Kaduna: Wasu ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Mutane Sama Da 80 A Wasu Kauyuka

Akalla mutane 87 aka yi garkuwa da su a wasu kauyuka guda biyu lokacin da ‘yan bindiga suka kai wani hari Kaduna.
Kauyukan su ne Gangere da Aguna da ke karkashin gundumar Kufana ta karamar hukumar Kajuru a jihar ta Kaduna.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Litinin din nan. Ba’a bayyana cikakkun bayanai game da yadda lamarin ya faru ba, amma ba a san inda wadanda lamarin ya shafa suke ba.
Wani shugaban yankin kuma jagoran matasa, Ben Yuhana, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce, “’yan bindigar sun shiga kauyukan Gangere da Aguba da ke gundumar Kufana Chiefdom a karamar hukumar Kajuru, inda suka yi garkuwa da mutane 87 a tsakanin daren jiya zuwa safiyar yau Litinin.”
Kawo yanzu dai gwamnatin jihar ba ta bayar da wata sanarwa a hukumance game da lamarin ba, yayin da kwamishinan ma’aikatar tsaron cikin gida da harkokin cikin gida Mista Samuel Aruwan bai mayar da martani kan sakon da jaridar Daily Trust ta aike masa ba.
Da aka tuntubi Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan, ya ce zai yi bayani, idan ya samun cikakken bayani kan lamarin, sai dai bai yi hakan ba har zuwa lokacin hada wannan labarin.