Featured
Harkokin Sun Tsaya A Jami’o’in Gwamnati, Yayin Da Yajin Aikin SSANU Da NASU Ya Shiga Kwana Na Biyu

Yayin da yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai da mambobin kungiyar SSANU da NASU ya shiga rana ta biyu a yau Talata, tare da dakatar da ayyukan da ake yi a harabar jami’o’in kasar.
Gwamnatin tarayya ta soki matakin da ma’aikatan da ba na ilimi suka dauka, tana mai cewa janye ayyukan nasu ya saba wa tanadin sashe na 18 na dokar hana tada zaune tsaye.
Kungiyoyin biyu sun fara yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai a ranar Litinin din da ta gabata, kan hana su albashi tare da ma’aikatan da ke aiki a rajista, tsaro, da al’amuran dalibai sun janye ayyukansu.
Gidan Talabijin na Channels ya rawaito cewa babu wani abu da ke tafiyar a harkokin mulki a cikin jami’o’in gwamnati a fadin kasar nan, yayin da gidajen kwanan dalibai ke kulle tare da katse wutar lantarki.
SSANU da NASU dai na zanga-zangar kin biyan albashin da gwamnatin tarayya ta yi. Kungiyoyin biyu sun caccaki gwamnatin tarayya kan biyan albashin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta hana a yi yayin da ta yi watsi da kungiyoyin da ba na ilimi ba.