Featured
Kaduna: Dakarun Sojoji Sun Kubutar Da Mutane 16 Da Aka Sace A Kajuru

Dakarun rundunar sojojin kasar nan shiyya ta daya da ke jihar Kaduna sun yi nasarar dakile wani yunkurin yin garkuwa da wasu ‘yan bindiga da masu tayar da kayar baya suka yi, tare da kubutar da mutanen da suka yi garkuwa da su a unguwar Tantatu da ke karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.
Daraktan yada labaran rundunar Manjo Janar Onyema Nwachukwu ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Litinin.
A cewarsa, sojojin sun yi amfani ne da bayanan sirri da aka samu a daren Lahadi inda suka bibiyi maharan da suka yi awon gaba da wasu mutane a kauyen.
Sanarwar ta kara da cewa, “Da isar su wurin da lamarin ya faru, sojojin sun bi sawun ‘yan ta’addan, inda suka yi musayar wuta tare da ceto mutane 16 da aka yi garkuwa da su.”
Bayan ceton, babban hafsan sojin kasa Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya yaba wa sojojin bisa nasarar da suka samu, inda kuma ya umurce su da su kasance cikin taka-tsan-tsan a ci gaba da gudanar da ayyukan yaki da ‘yan tada kayar baya don ‘yantar da dukkan yankunan kasar nan.