Connect with us

Featured

Rundunar ‘Yan Sanda Ta Musanta Kai Hari Kan Masu Sallar Dare A Zamfara

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta ce wasu ‘yan bindiga sun kai hari tare da kashe wani mutum mai suna Ashiru Nagoma tare da yin garkuwa da matarsa ​​da makwabcinsa a Buluku da ke wajen karamar hukumar Gusau a jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Yazid Abubakar, ne ya tabbatarwa da jaridar PUNCH a ranar Talatar nan.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da wani kwararre kan harkar tsaro mazaunin Maiduguri, Zagazola Makama ya wallafa a shafin X (Twitter) wanda ya yi tsokaci kan cewa ‘yan bindiga sun shiga garin Gusau, sun yi awon gaba da wasu masallata a wani masallaci lokacin da suke sallar tsakiyar dare da misalin karfe 2.

“Abun bakin ciki. Da tsakar daren ranar Talata da misalin karfe 0200, ‘yan bindiga sun kutsa cikin garin Gusau inda suka yi awon gaba da wasu masu ibada a wani masallaci a lokacin da suke gudanar da sallar tahajjud (tsakar dare),” kamar yadda ya rubuta.

Sai dai kuma da yake magana kan lamarin, Abubakar ya jaddada cewa marigayi Nagoma ya tsallakewa harin da ‘yan bindigar suka kai musu, inda su kuma suka kashe shi suka yi awon gaba da matarsa ​​da makwabcinsa.

“’Yan bindigar ba su kai hari masallacin ba. Suna da manufa, kuma mutumin aka kaiwa hari. An sace matarsa ​​da makwabcinsa.

“Tawagar mu na wurin a halin da ake ciki, kuma tana kokarin ganin an gano wadanda suka aikata laifin tare da kubutar da wadanda aka sace. Ana kuma ci gaba da gudanar da bincike,” inji shi.

A watan Fabrairu ne dai jaridar PUNCH ta ruwaito cewa, ‘yan bindiga sun yi awon gaba da wasu masallata a daya daga cikin masallatan garin Tsafe, shedikwatar karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.

Wani dan yankin mai suna Garba, ya shaidawa manema labarai cewa ‘yan bindigar sun mamaye masallacin ne da misalin karfe 5 na safe a lokacin da mutane ke shirin fara sallar asuba.

Garba ya ce, “Yau alhamis za mu fara sallar asuba, kwatsam sai ga su (’yan bindiga) suka shiga masallaci suka umarci kowa ya fita ya bi su.

“Kowa ya yi kokarin tsira, amma ‘yan bindigar sun tare ko’ina kuma suka gargade mu cewa za su kashe duk wanda ya yi yunkurin guduwa.”

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet